Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, malaman makarantun book da kuma na adini kimanin 170 ne suka shiga gasar kur’ani mai tsarki ta malaman makarantu.
Wannan gasa dai tana daga cikin wadanda ak gudanawa da zaran an kammala azumin watan Ramadan mai al’farma a kasar, a karkashin ma’aikatar ilimi da kuma ma’aikatar kula da harkokin addini.
A wanann karon baya ga harda, an kara tafsiri ayoyin kur’ani da kuma hadisan ma’aiki.
Tun a cikin shekara ta 1974 ne aka fara gudanar da wannan gasa a kasar ta Bahrain, da take samun karbuwa matuka daga malaman makarantu.